• Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa
    Jan 8 2025

    A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su.

    Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su.

    Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance?

    Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi makamantansu shirin Daga Laraba na wannan makon zai binciko

    Show More Show Less
    28 mins
  • Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka
    Jan 1 2025

    A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.

    Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi.

    Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka.

    Show More Show Less
    28 mins
  • Dalilan Da Suka Sa Wasu Darikun Kirista Basa Bikin Kirsimeti
    Dec 25 2024

    A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti.

    Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na kirsimeti ba.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan wannan batu don gano dalilan da suka sa wadannan dariku basa bikin kirsimeti.

    Show More Show Less
    28 mins
  • Yadda Shara Ke Neman Binne Manyan Biranen Najeriya
    Dec 19 2024

    Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli.

    Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasirinta a kan lafiyar jiki da ta muhalli.

    Show More Show Less
    28 mins
  • Me Nasarar Da John Mahama Ya Samu Ke Nufi Ga kasar Ghana
    Dec 11 2024

    A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata.

    Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zaiyi Nazari ne kan nasarar da John Mahama ya samu a zaben kasar Ghna da kuma kalubalen da zai iya fuskanta a shekara daya na farkon wa’adin sa.

    Show More Show Less
    30 mins
  • Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Kishin Kabila Fiye Da Kasa
    Dec 4 2024

    Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu.

    Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba.
    Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin kasar da suke da shi.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan wannan batu.

    Show More Show Less
    32 mins
  • Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro
    Nov 27 2024

    Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan.

    Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe.

    Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’an tsaro dake taimaka wa jami’an tsaron gwamnati wajen dakile haren haren da yan ta’adda ke kaiwa a wasu yankunan kasar nan.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zaiyi duba ne kan wannan batu.

    Show More Show Less
    30 mins
  • Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya
    Nov 20 2024

    An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.

    A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai
    Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata.
    Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar.

    Show More Show Less
    25 mins