• Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
    Jan 9 2025

    Send us a text

    A wannan zamani, ’yan Najeriya da dama ba sa samun wadataccen abinci a yini.

    Magidanta da dama, musamman, sun tsallake sun bar iyalansu sun shiga bariki don neman na sanyawa a bakin salati.

    Mene ne dalilin hakan, kuma yaya za a yi a kauce wa fadawa cikin irin wannan yanayi?

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halin da galibin ’yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki na rashin samun abinci yadda ya kamata

    Show More Show Less
    26 mins
  • Amfanin Komawa Makaranta A Ranar Da Aka Bude Bayan Hutu
    Jan 7 2025

    Send us a text

    Malamai na dauri sun karantar da cewa idan mutum ya bar karatu na kwana daya, karatun zai bar shi tsawon mako guda; idan ya bar karatu mako guda, karatun zai bar shi wata guda.

    Sai dai a yau, a duk lokacin da aka ce an koma makaranta bayan hutu, a kan samu rashin komawar dalibai a ranar da aka koma – a wasu lokutan ma, har da malamai.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari tare da bayar da shawarwari ne a kan amfanin komawar dalibai makaranta a ranar da aka bude ta.

    Show More Show Less
    21 mins
  • Yadda Ma’aikata Za Su Daina Jira Kafin Shigowar Albashin Watan Janairu
    Jan 6 2025

    Send us a text

    A duk lokacin da aka ce an biya albashi, yanayi kan sauya ga masu karba har da masu sana’oi a kasuwanni da kananan shaguna a unguwanni.

    Sai dai watan Janairun ko wace shekara kan zo da kalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma karar da shi a kan bukukuwan da watan kanzo dasu.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda masu aikin albashi za su kauce wa shiga halin ni-’ya-su kafin biyan albashin watan Janairu

    Show More Show Less
    30 mins
  • “Makomar Bangaren Ilimi A 2025 Tana Cikin Hadari”
    Jan 3 2025

    Send us a text

    Ga mai son yin nazari a kan makomar bangaren ilimi a Najeriya a 2025, tanade-tanaden Kasasfin Kudi na bana ka iya zama manuniya.

    A kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na 2025 dai, an ware wa bangaren ilimi sama da naira tiriliyon uku.

    Wannan ne kuma karo na farko da bangaren ya samu irin wannan gata.

    Sai dai da alamu hakan bai yi wa malaman makaranta da masu ruwa da tsaki dadi ba.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan alkiblar da bangaren ya fuskanta a shekarar 2025

    Show More Show Less
    25 mins
  • Halin Da Matsalar Tsaro Ya Jefa Wasu Alummomin Arewa A Shekarar 2024
    Jan 2 2025

    Send us a text

    A cikin ‘yan shekarun nan, matsalar tsaro ta kasance babbar kalubale a Arewacin Najeriya. Musamman a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da kuma jihar Sakkwato. Daga matsalar ‘yan fashi zuwa ta’addanci, yankin ya fuskanci barazanar tsaro daban daban.

    Duk da irin wadannan kalubale, mutanen wadannan yankuna sun nemo wasu hanyoyi daban-daban na jure irin wadannan matsaloli. Taimakon ‘yan sa kai a wasu al’ummomi ya taka muhimmiyar rawa, inda kungiyoyin sa-kai da kuma tsare-tsaren gwamnati suka yi tasiri a wasu wurare.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan wannan batu.

    Show More Show Less
    23 mins
  • Yadda Takkadama Ta Kanannande Siyasar Kananan Hukumomi A Shekarar 2024
    Dec 31 2024

    Send us a text

    Zabukan Kananan hukumomi na cikin al’amuran da suka dauki hankali a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2024.

    Duk da an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu daga cikin jihohin Najeriya, zabukan kananan hukumomi na cikin batutuwan da ’yan Najeriya suka fi zantawa a kai, mai yiwuwa saboda ganin da ake yi cewa wadannan zabukan sun fi shafar alumma kai tsaye.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi waiwaye a kan kurar da wasu daga cikin zabubbukan kananan hukumomi suka tayar a 2024

    Show More Show Less
    25 mins
  • Yadda ’Yan Najeriya Suka Jure Wa Matsin 2024
    Dec 30 2024

    Send us a text

    Tun bayan rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayun bara ne dai ’yan Najeriya suke ta kokawa da matsin tattalin arziki sakamakon wasu tsare-tsare da manufofi da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da su.

    Wadannan manufofi sun hada da janye tallafin man fetur da kyale kasuwa ta yi halinta a kan darajar Naira da janye tallafin wutar lantarki da sauran su.

    Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi tsokaci ne a kan jimirin da ’yan Najeriya suka yi a shekarar.

    Show More Show Less
    27 mins
  • Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato
    Dec 27 2024

    Send us a text

    A baya bayan nan ana cigaba da samun hare hare da sojoji ke kaiwa kan fararen hula kamar yadda wasu suka bayyana.

    Ko A shekarar da ta gabata, rundunar sojin kasar nan ta kai wani hari garin Tudun biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda harin yayi sanadiyyar mutuwar gomman mutane.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi duba ne kan harin da rundunar sojin kasar nan ta kai a jihar Sakkwato

    Show More Show Less
    22 mins